June 8, 2025
Breaking News
No result!
Sunday, 14 February 2016

Coconut masa


Ingredients
Farar shinkafa
Yeast
Madara
Albasa
Kwakwa
sugar
Method
Ki wanke shinkafarki ki yanka albasa in babba ne kisa rabi in karamine kisa guda daya seki kai a markada mishi, kafin Nan zaki jika shinkafar da yamma ne ya kwana se ki kai nikar washe gari da yamma, in an niko seki ajiye zuwa dare, kisake dafa farar shinkafar ta dahu sosai seki bari ya dan huce amma ba yayi sanyi gaba daya ba, yanda zaki iya sa hanun ki seki zuba cikin kullin markaden nan kizuba yeast cokali daya babba daya ki dama su sosai saiki rufe ya kwana xuwa gobe, dama kin jika kanwanki saboda tsami, seki kankare kwakwa ki xuba yanda zai wadata kisa madara da sugar sai dandana inda tsami kisa kanwar kadan har yai daidai shikenan seki dinga soyawa
Fat Flush Water
1 grapefruit, sliced
1 tangerine, peeled
1/2 cucumber
Mints leaves
Soak it overnight and drink it all day; you can add ice to chill.
This water flushes fat away. Drink it for 4-8 weeks and experience differently.
Dafarko zaki sami dankalin ki feraye shi sai ki wanke kizuba a tukunya ki zuba ruwa da dan gishiri ki dafa yanda banzai rushe ba, sai ki sauke ki aje a guri daya ,sai ki sami minced meat din ki zuba a bari daya na dankalin sai ki Sa dayan kirufe ,sannan sai ki sami toothpick ki soka atsakiya ,sai ki dora man ki awuta ,nan kuma kin fasa kwai kar ki kada sosai dan kar ya tsinke, sai ki tsoma dankalin aciki sai ki soya shi.@meena Kurawa.✒
GANISHED FRIED CHIPS WITH LIVER
Ingredients
©Dankali turawa
©Liver
©Tarugu, tattasai n tumatir
©Sweet pepper n Cabbage
©Onions n garlic
©Maggi/salt
©Curry n thyme
METHOD
Da farko zaki fere dankalin sai ki yankashi cubes sai ki soya ki ajiye a gefe, ki yanka liver dinki kamar size na dankalin ki tafasa with seasonings dinki ki aje a gefe, ki slizin onions cabbage da sweet pepper ki aje a gefe, ki jajjaga attaruhu tattasai tumatir n garlic, sai ki daura mai kadan a wuta sai ki zuba jajjagen ki, sai ki kawo liver dinki ki zuba ki gauraya ya dan soyu kamar stew kada ki soye su sosai, sai ki zuba seasonings dinki sai ki kawo chips dinki ki zuba tare da su slize onions dinki, ki dan jujjuya ki soya su 4 lyk 4mins, shikenan aci dadi lfy. By kareem's special kitchen🍹🍸🍲
DADIN TUKUNYA
INGREDIENTS:
1. Nama
2.Albasan, tafarnuwa
3.Mai,'Kuli
4.Maggi, Gishiri
5.Citta, kanunfari/masoro, curry, da sauran kayan kamshi.
PROCEDURE:
Da farko ki gyara namanki ki yanka shi irin shape din da kike so, ki wanke ki dora a wuta, ki sa maggi, gishiri curry, citta, sai ki zuba dakakken kanunfari da masoro kadan.
Ki rufe ki barshi yayi ta dahuwa, idan ruwan yayi kasa, sai ki jajjaga albasa da tafarnuwa ki zuba a ciki ki jujjuya, ki barshi ya cigaba, sai ya dahu lugub ruwan ya kusa konewa sai ki gutsuri naman kiji yanayin maggi da gishiri, idan da bukatar Kari sai ki kara, sai ki zuba mai aciki ya cigaba da soyuwa, ki daka kulinki ki juye a ciki ya cigaba da soyuwa kamar na minti 5, ki yanka albasa mai yawa sala-sala kuma sirara, sai ki zuba cikin tukunyar naman ki juya sosai ki rufe minti 2, ki sauke ba aso albasar tarabe kada ta dahu anaso a dinga taunawa tana garas-garas.
Potato Sandwich
Ingredients
Dankali
Nikakken nama
Kwai
Maggi
Curry
Albasa
Tafarnuwa
Mai
Method
Zaki feraye dankali sai a raba shi biyu a tsaye. Haka za a yi da sauran dankali byan an gama sai a dafa shi da curry na 10mins. Sai a sauke ajiye gefe daya.
Za a zuba nikakken nama a kwano ko roba sai a sa maggi gishiri d curry da kuma albasa da tafarnuwa da aka jajjaga sai a cakuda sosai. In komai ya ji sai a soyashi daidai ci ajiye gefe daya.
Sai a dinka daukan bari dayan na dankalin ana saka naman a saman sannan a rufe da daya barin dankalin.
Sai a kada kwai a kwano a sa maggi da albasa sai a dinka daukan dankalin ana sawa a cikin kwai sannan a soya a mai mai zafi.

0 comments :

Post a Comment

Back To Top